<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><author>Luther, Martin (1483-1546)</author>
<title>Allahnmu Garu Mai Ƙarfi LW372</title>
<lyrics>[V1]
 1) Allahnmu garu mai ƙarfi
 Makami mai nasara
 Ko'ina shi ne cetonmu
 Kariyarmu ta kirki
 Maƙiyi mugun ne
 In ya ƙara ƙarfi
 Duka banzane
 Mai magabci ya iya
 Allah ya fi ƙarfinshi

[V2]
 2)Mu kaɗai ba za mu iya
 Ƙarfinmu ba ya isa
 Akwai jarumi yin yaƙi
 Dominmu yana ta yi
 Wanene shi kariyar
 Kai ne mai cetonmu
 Allah mai Runduna
 Kabilu kassassu
 Sun sani da mai ceto

[V3]
 3)Ko Shaiɗan ya yi ta tarko
 Don ya cuci Ekklisiya
 Ƴar Sion ta wuce Hades
 Bisan dutsi ta zauna
 Ta riƙe famarta
 Ba zancen mutuwa
 Da Shaiɗan zai kawo
 Don rushe gininta
 Maganar Allah ta isa

[V4]
 4)Faɗi maganar nasara
 Cikin dukan tsanani
 Sauko mana daga sama
 Albarkunka ya Allah
 Ko an mana ƙwace
 Ko ma an kashe mu
 Mine muka rasa
 Alherinka ya fi
 Mulkinka na mutanenka.</lyrics>
<hymn_number>372</hymn_number>
</song>